Bikin Sallah: Hatsarin Mota ya salwantar da rayuka 2, Mutane 8 sun jikkata a jihar Ogun


Legit HausaTabbas mutane biyu sun riga mu gidan gaskiya yayin aukuwar wasu hadurra biyu daban daban a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan cikin birnin Abeokuta na jihar Ogun a ranar Talata ta bikin karamar Sallah. Kwamandan hukumar kula da manyan tituna reshen jihar Ogun, Mista Clement Oladele, shi ne ya bayar da shaidar tabbacin wannan mummunan lamari cikin wata sanarwa yayin ganawar sa da manema labarai a ranar Laraba
.
Oladele ya ce hatsarin farko ya auku da misalin karfe 4.52 na safiyar Talata a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan daura da gidan man fetur na AP a garin Shagamu. A yayin da aukuwar hatsarin na biyu da ya maimatu akan wannan hanya ta wakana da misalin karfe 3.54 na Yammacin Talata, rayukan Mutane biyu sun salwanta yayin da mutane takwas suka jikkata. 

An garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibitin Idera dake garin Shagamu yayin da aka killace gawawwakin wadanda suka riga mu gidan gaskiya a asibitin koyarwa na jami'ar Olabisi Onabanjo. Hukumar kula da lafiyar manyan hanyoyi ta FRSC na ci gaba da gargadin masu ababen hawa da suka tabbatar da kiyaye ka'idojin tuki yayin gudanar safarar su musamman a wannan lokuta na shagulgulan Sallah.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN