Legit Hausa
Sanata mai wakiltan yankin Zamfara ta tsakiya, Kabiru Garba
Marafa, ya bayyana cewa bai yi danasanin duk wani mataki da ya dauka na cewa
lallai APC reshen jihar Zamfara bata gudanar da zaben fidda gwani ba a watan
Oktoban shekarar da ya gabata.
Marafa wanda karar da ya shigar kotu yayi sanadiyar soke
dukkanin zaben fidda gwanin da jam’iyyar ta gudanar a jihar, yace mutanen
Zamfara na farin ciki da hukuncin kotun koli da ya kori dukkanin zababben yan
APC a jihar.
Da yake Magana a taron bankwana na majalisar dattawa na takwas
a jiya Alhamis, 6 ga watan Yuni, Marafa yace koda dai bai so ace jam’iyyar
adawa ta PDP ta amfana daga matakinsa ba, tuna ya amince da hukuncin. “Ban yi
danasani kan abunda nayi ba. An haife ni ne domin nayi yaki, kuma zan ci gaaba
da yaki. Mutanen jihar Zamfara sun yi farin ciki da abunda ya faru,” inji shi.
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi