Legit Hausa
An samu gawar wata yarinya mai shekaru 16 da haihuwa wacce aka
kashe kuma aka jefar da ita cikin daji. DPO mai kula da ofishin yan sandan
karamar hukumar Mashi a jihar Katsina, Garba Talawai ne ya aikata laifin kisan.
Ita dai wannan yarinyar da aka kashe, ta kasance yar aiki ne wurin budurwar DPO
mai suna Safiya Danyaya.
Majiyar Daily Nigerian ta tattaro rahotanni cewa, DPOn yayi
kokarin zubar wa yarinyar cikin da take dauke da shi ne wanda hakan yayi
sanadiyar mutuwarta. “ A lokacin da ya lura cewa lallai ta mutu, sai ya nemi
taimakon wani dan uwansa dan sanda na ya taimaka masa wurin jefar da gawar.”
Inji wata majiyar da ta buqaci a boye sunanta. Tuni
Kwamishinan yan sandan Katsina, Sanusi Buba, ya sa aka kama Talawai bayan da
rahotanni suka tabbatar da cewa ya aikata laifin kisan kai. A wani zance da ya
fito daga bakin mai magana da yawun hukumar yan sandan jihar Katsina, Gambo Isa
ya ce: “ An samu gawar Rabi a cikin wani daji dake hanyar zuwa Mashi ranar
Alhamis.”
Kakakin hukumar yan sandan ya cigaba da cewa: “ Safiya wacce
ita ce budurwar Talawai ta bamu labarin cewa yar aikin ta bata ne tun ranar
Laraba, kuma ta sanar da DPO kan hakan.” A cewar Safiya“ Rabi tayi hijira ne
bayan da na lura cewa tana dauke da juna biyu, wanda ya sanya na fara matsa
mata.” Isa ya tabbatar mana da cewa a yanzu haka DPO da buduwarsa na hannun
‘yan sanda domin binciken haqiqanin musabbabin kisa
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Tags:
TSARO