Legit Hausa
Wata dalibar jami’ar Benin (UNIBEN), Christabel ta kashe
kanta a dakin kwananta dake unguwar Newton, Ekosodin a garin Benin bayan ta sha
guba. Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa, marigayiyar ta sha maganin kashe
kwari bayan ta hada shi da lemun kwalba, ta kuma bar wasika inda ta bayyana
cewa zata kashe kanta saboda saurayinta ya rabu da ita. Amman wata majiya ta
kawo cewa an gano ledan sabulun wanki a inda aka tsinci gawarta.
Haka zalika, a wani rubutu a shafin zumunta daga wata
ma’aikaciyar UNIBEN, an rahoto cewa wasikar, wanda a halin yanzu ya ke a hannun
yan sanda a ofishin yan sanda a Ugbowo, an rubuta ta ne zuwa ga mutane biyu,
sannan kuma an gayyace su zuwa ofishin yan sandan don amsa tambayoyi.
Rubutun yayi ikirarin
cewa ba wait a kashe kanta saboda matsalar da ta samu da masoyinta bane kawai
illa wasu al’amuran da ta kasa magancewa a tsakaninta da wadannan mutane biyun
da ta ambata a wasikar.“Wasikar bai bayyana abunda ya faru ba tsakaninta da
mutane biyun da ta ambata, wannan dalilin ne yasa yan sanda suka gayyace su
domin su bayyana dalilin da yasa marigayiyar kashe kanta,” cewar rubutun.
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Tags:
NISHADI