An zabi Ahmed Lawan shugaban majalisar dattawan Najeriya

BBCHausa

Bayan zaben Sanata Ahmed Lawan a matsayin shugaban majalisar dattawan Najeriya, yanzu za fara zaben mataimakinsa.
An bayyana Sanata Ahmed Lawan a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban majalisar dattawa, inda ya samu kuri'a 79, yayin da Ndume ya samu 28. Kuri'a 107 aka kada gaba daya.
Tuni aka fara kirga kuri'un da aka kada a zaben shugaban majalisar dattawa tsakanin Ahmed Lawan da Ali Ndume.

Wasu daga cikin sanatocin da ke goyon bayan Ahmed Lawan na gaisawa da shi bayan da aka fara ware kuri'un da aka kada. Alamu na nuna cewa kamar na sa sun fi yawa.
Sanata Ali Ndume da kuma Ahmed Lawan suna jiran sakamakon zaben da aka kada, inda ake tantance kuri'u.
An kammala kada kuri'a a zaben shugaban majalisar dattawa. A yanzu za a fara ware kuri'un da aka kada domin tantance su

DAGA ISYAKU.COM Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN