An kama wani malamin makarantar Allo da ya ke hada kai da Almajiransa suna satar mutane


Legit Hausa

Rundunar 'yan sandan jihar Osun ta kama wani malamin addinin Musulunci mai suna Alfa Majid Olore, bayan an gano wani gida da yake satar mutane yana boye a Ibadan babban birnin jihar Oyo.
Jaridar Independent ta bada rahoton an kama Alfa tare da matarsa da 'ya'yansa da kuma sama da Almajiransa 55, wadanda ke zama a Ita Baale a cikin garin Ibadan. Haka kuma kimanin mutane 20 rundunar 'yan sanda suka kama a yankin Ita Baale.

A cewar wani wanda lamarin ya faru akan idonsa, mutanen da ake zargin an kulle su a ofishin 'yan sanda na Agugu dake garin Ibadan. Mutumin ya ce, "Shi dai ya san yaga 'yan sanda sun zo gidan malamin dake unguwar Ita Baale, inda suka kama shi da matarsa da 'ya'yansa da kuma Almajiransa guda 55, sannan kuma an kama wasu mutanen suma a unguwar. 

Ban san ainahin abinda suka yi ba a lokacin, amma dai naga 'yan sandan na dukan Malamin kamar baza su barshi da rai ba, daga baya suka sanya mishi ankwa." A lokacin da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar, Mista Olugbenga Fadeyi, ya ce har yanzu hukumar tana bincike akan lamarin domin tabbatar da cewa zargin da ake yi gaskiya ne.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN