Legit Hausa
Hukumar
sojin Najeriya ta yi arangama da wasu masu yiwa yan bindiga leken asiri da masu
kai musu kayayyaki a kasuwan Burkusuma a karamar hukumar Sabon Birnin jihar
Sokoto.
Game da
cewar kakakin hukumar, Kanal Sagir Musa, ya ce dakarun sojin atisayen Operation
HARBIN KUNAMA III sun yi wannan kamu ne a harin bazatan da jami'an soji suka
kai wa yan bindigan cikin jihar Sokoto da kewaye ranar 23 ga Yuni, 2019.
Sun kai
harin ne bisa ga rahoton leken asirin da suka samu cewa yan leken asirin masu
garkuwa da mutanen sun shigo kasuwa siyayya.
Daga cikin
wadanda saka kama sune:
(1) Malam Ibrahim - Shahrarren mai kaiwa
yan bindiga labari da kuma amsan kudin fansa (ii) Mallam Ashiru Goni —
Shahrarren mai kaiwa yan bindiga kayayyaki ciki da wajen jihar Sokoto (iii)
Mamman Taratse — Shahrarren mai sayar da shanun sata a ciki da wajen jihar
Sokoto Hakazalika, jami'an sojin sun yi batakashi da da yan bindiga a kauyan
Magira bayan samun labari.
(2) An hallaka yan bindiga da dama kuma
an yi rashin soja daya. Ya ce kwamandan 8 Division, Manjo Janar Hakeem Oladapo
Otiki, a madadin babban hafsan soji Laftanan Janar Tukur Buratai, ya yabawa
sojin kan jajircewan da sukayi wajen samun wannan nasara.
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Tags:
BIRNIN-KEBBI