Ali ya ga Ali: Sarkin Kano Sanusi ya hadu da Ganduje a masallacin idi bayan ya ja shi Sallah (hoto)


Legit Hausa

A yau Talata, 4 ga watan Yuni ne daukacin al’umman Musulmi a sassa daban-daban na duniya suka gudanar da bikin Eid-el Fitr bayan kammala azumin watan Ramadana. Jama’a sun tunkari masallatai daban-daban domin cika ibadunsu na Ramadana ta hanyar godiya ga Allah madaukakin Sarki. 

Hakan ce ta kasance a jihar Kano inda Sarakuna, manyan yan kasuwa, manyan yan siyasa ciki harda Gwamna Abdullahi Umar Ganduje suka halarci Sallar idi. Sarki Muhammadu Sanusi II ne ya jagoranci bayar da sallar idi a babban masallacin idi da ke Kofar Mata a Kano. 

Bayan sun idar da Sallah an gano Gwamna Ganduje tare da Sarkin Kano suna Musabaha cike da farin ciki da walwala. Wannan shine karo na farko da shugabannin ke haduwa tun bayan kunnowar rikicin masarautar jihar, inda gwamnan ya kacaccala ta zuwa gida biyar. 

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Fadar mai martaba sarkin Kano ta musanta zargin da hukumar yaki da rashawa da sauraron koke koken jama’a ta jahar Kano keyi mata tare da mai martaba Sarki Muhammadu Sunusi II na yin bindiga tare da almubazzarantar da naira biliyan 3.4.
Legit.ng ta ruwaito walin Kano, Alhaji Mahe Bashir ne ya bada wannan kariya ga masarautar a ranar Litinin, 3 ga watan Yuni, inda yace zarge zargen da ake yi ma masarautar basu da tushe balle makama, sa’annan ya bayyana daki daki yadda masarautar ta kashe kudadenta.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN