Akwai tarin matsaloli a tsarin zaben Najeriya – Tarayyar Turai ta yi bankada


Legit Hausa

Rahotanni sun kawo cewa tawagar tarayyar Turai da suka sanya idanu akan zaben Najeriya da ya gabata, sun ce akwai bukatar canja tsarin zaben kasar bayan sun bankado wasu tarin matsaloli a zabukan 2019 wanda ya gudana. Tawagar EU din sun bayyana hakan ne a yayinda suke gabatar da rahotonsu na karshe kan zaben Shugaban kasa, na yan majalisa da kuma na gwamnoni wanda aka gudanar wasu yan watanni da suka gabata.

Babbar jami'ar da ta jagoranci tawagar Maria Arena ta ce an bata gaskiyar tsarin zaben Najeriya na 2019 sakamakon rikici da barazana. A cewarta an samu matsaloli daga bangaren tsaro, matsalar jigilar kayan zabe da kuma rashin fitowar al’umma.

Daga cikin shawarwarin da rahoton ya bayar, sun hada da inganta tsarin tattara sakamakon zabe, musamman tsarin da zai bayyanawa jama'a sakamakon kafin sanar da shi. Babu dai wani martani da ya fito daga bangaren hukumomin Najeriya game da rahoton na Tarayyar Turai.

Rahoton na zuwa bayan watanni uku da aka gudanar da zaben shugaban kasa wanda shugaba Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC ya lashe. Tarayyar Turai ta dora laifin matsalolin da aka samu akan jam'iyya mai mulki, kan rashin tsawatarwa ga magoya bayanta da rashin daukar matakan kaucewa cin karo da matsalolin.

Ta ce an yi amfani da karfin mulki a bangarorin Tarayya da jiha. Kuma dakatarwar da aka yi wa Alkalin alkalan kasar, makonni kafin a gudanar da zabe ya saba wa 'yancin shari'a a Najeriya. Tarayyar Turai ta bukaci a gaggauta sauya tsarin zaben Najeriya saboda matsalolin da ta gano kafin zaben 2023.
 

DAGA ISYAKU.COM Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN