Ahmad Lawan ya aiwatar da aikin farko a matsayin Shugaban majalisar dattawa


Legit Hausa

Sanata Ahmad Lawan a ranar Alhamis, 13 ga watan Yuni ya gudanar da aiki na farko a matsayin sabon Shugaban majalisar dattawan Najeriya, inda ya rantsar da Sanata Rochas Okorocha a matsayin mai wakiltan yankin Imo ta yamma a majalisar. 

Taron ya gudana ne jim kadan bayan majalisar dattawa ta gabatar da addu’o’i, da sauransu a zauren majalisar da ke Abuja. Lawan ya rantsar da Okorocha a zauren majalisar da misalin karfe 10:39 na safe. Legit.ng ta ruwaito cewa a ranar Talata, 11 ga watan Yuni ne yan majalisar suka zabi Lawan da Sanata Ovie Omo-Agege a matsayin Shugaban majalisar dattawa da mataimakinsa. 

A baya mun ji cewa Sanatan Borno, Ali Ndume, a ranar Laraba, 12 ga watan Yuni yace ya ajiye lamarin kaye da ya sha a hannun Ahmed Lawan wajen neman kujerar shugabancin majalisa a kefe. Mista Ndume yayi takara da sabon Shugaban majalisar dattawa, Mista Lawan, a lokacin rantsar da majalisar dattawa ta tara wanda aka gudanar a ranar Talata, 11 ga watan Yuni. 

Da yaki jin duk wani rarrashi da aka yi masa domin ya janye, Mista Ndume yace lallai sai yayi takarar wannan kujera. Sai dai ya sha kaye a hannun Lawan bayan anyi zaben inda ya samu kuri’u 28.

DAGA ISYAKU.COM

 Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN