Abubuwa 5 da kungiyar Yarbawa ta roki Shugaba Buhari

Legit Hausa

A jiya Talata 25 ga watan Yuni, 2019 ne Kungiyar Yarbawa ta Afenifere ta ziyarci Shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa dake Abuja tare da mika masa kokon baransu na wasu abubuwa guda biyar (5).
Kungiyar wacce Cif Ayo Fasanmi ke jagoranta ta fada wa Shugaban kasa cewa wadannan abubuwan da suke roko guda biyar idan har aka samar da su, za su taimaka wajen rage kalubalen da kasar nan ke fuskanta.
Wadanda suka halarci wannan ganawa sun hada da; Bola Ahmed Tinubu, Segun Osoba, Abiola Ajimobi, Sanata Adebayo Adeyeye, Cif Kemi Nelson, Laoye Tomori, Solomon Akindele, Elder Yemi Alade, Mutiu Are da dai sauransu.
Kungiyar ta gabatar da wata takarda wadda, Sanata Olabiyi Durojaiye ya karanta a madadin kungiyar.
Ga abinda wannan takardar tasa ta kunsa kamar yadda yana Olabiyi ya karanto ta: “ Ranka ya dade, ka muna neman ka bamu izinin gabatar da kokon barar mu mai dauke da abubuwa guda biyar.
“ Tsaro: Akwai buqatar gwamnati ta dauki matakai kwarara wajen magance matsalolin tsaron kasar nan. A tamu shawarar muna ganin salon daukar ‘yan sanda daga kananan hukumomi 774 dake fadin Najeriya zai taimaka kwarai da gaske.
“ Ilimi: Samar da ilimi kyauta wanda kuma yake wajibi. Wasu daga cikin sassan kasar nan sun gwada gudanar tsarin ilimi na bai daya kyauta kuma hakan ya haifar da da mai ido.
“ Karfafa matasa: Samarwa matasa abin yi, wannan abu na da matukar muhimmanci saboda zai ba matasa damar dogaro ga kawunansu. Sana’o’in da za’a iya koyar da su, sun shafi fanni amfani da na’ura mai amfani da kwakwalwa wato ICT da ma wasu bangarorin ta yadda za a rage zaman banza.
“ Hadin kan kasa guda daya: Babu abinda zamu iya cinma ba tare da hadin kai ba a kasar nan. A don haka kasancewar Najeriya tsintsiya madaurinki daya nada muhimmanci kwarai da gaske.
“ Harkar lantarki: Mun riga da mun yaba da irin kokarin da gwamnatin nan ke yi a bangaren wutar lantarki. Akwai buqatar karin qaimi domin samar da lantarki ya kasance ta wadata a kasar nan.” Kamar yadda Olabiyi ya fadi.
Shi kuwa Shugaban kasa Muhammadu Buhari da yake amsa wa jawabin na su, cewa yayi “zamu duba wannan rokon naku kamar yadda nayi alkawari a lokacin kamfe na 2019.”
DAGA ISYAKU.COM Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN