Legit Hausa
Hukuncin kotun koli na soke kuri'un jam'iyyar APC a zaben
gwamna na shekarar 2019 a jihar Zamfara ya sanya jama'a da dama murna a garin
Gusau babban birnin Jihar Zamafara kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Masu babbura da dama suna ta yawa a titunan Gusau suna
yabawa hukuncin kotun yayin da suke dauke da fostocin dan takarar gwamnan na
jam'iyyar peoples Democratic Party ( PDP) Dr Bello Mutawalle Maradun.
Mazauna garin Gusau kuma sun bayyana mabanbanta ra'ayoyi
game da hukuncin babban kotun inda wasu da yawa cikinsu su kayi fatan alheri ga
gwamnatin da za ta kama aiki nan ba da dadewa ba. "Ina fatan sabuwar
gwamnatin za ta inganta rayuwar mutane.
Banyi mamakin hukuncin kotun ba duba da abubuwan da suka
rika faruwa tun daga lokacin da aka fara zabukkan cikin gida zuwa yanzu,"
inji wani magidancin mai suna Aliyu Hussain.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi