Zamana a gidan yarin kasar Saudiya –Zainab Aliyu


Legit Hausa

Zainab Aliyu mai shekaru 22 da haihuwa ta tsinci kanta cikin wani maiwuyacin hali inda aka kama jakarta da miyagun kwayoyi a kasa mai tsarki. Hukuncin wannan laifi kuwa shine kisa a bisa dokokin kasar ta Saudiya.Bayan an dauki tsawon lokaci anata kai ruwa rana yayin bincike da kuma tattaunawa tsakanin kasashen Najeriya da Saudiya, an samun gano gaskiyar lamarin cewa ba ita keda mallakar kwayoyin ba cusa mata akayi cikin jakarta ba tareda sanin ta ba .

A ranar Litinin ta dawo gida Najeriya bayan ta kwashi tsawon watanni hudu a gidan kaso. Ga kadan daga cikin yadda tayi zaman gidan yarin kamar yadda ta shaidawa jaridar Daily Trust:

Jaridar Daily Trust: Shin ko za ki iya fada mana halin da kika tsinci kanki a gidan yarin Saudiya tsawon watanni hudu?

Zainab Aliyu: Mun kasance muna bacci nida mahaifiyata da yar uwata Hajara a dakin otal din muka sauka, kwatsam sai wasu jami’an tsaro larabawa tareda bakaken fata biyu sun fado mana. Suka tashe mu daga bacci suna tambayarmu akan jakar da muka baro dauke da kwayoyi a tashar jirgin saman Jiddah. Nan muka fada masu bamu da masaniya akan jakar da suke magana akai, sai suka sanar da mahaifiyata cewa zan bisu zuwa ofishinsu saboda jakar me dauke da kauyoyin sunana take dauke dashi.
Daily Trust: Akwai wanda ya sanar dake cewa za’a kai ki gidan yari?

Zainab: A’a babu wanda ya sanar dani. Ko bayan an kai ni can ma banyi tsammanin cewa gidan yari bane. Saboda ni har a raina nasan cewa ban aikata laifin komi ba. Daga baya na lura cewa tabbas gidan yari aka kawo ni. Nan suka bani daki, mu hudu ne a dakin a ciki na samu aron wayar salula na kira mahaifiyata. 

Daily Trust: Kin kuwa yi abokai a gidan yarin? 

Zainab: Eh nayi abokiya guda daya, yar kasar Habasha. Mun dade bamu magana saboda ita turanci kadan take ji ni kuma larabci kadan nakeji. Amma daga baya na iya larabci kwarai da gaske saboda haka muka fara magana da ita. Mun shaku da juna sosai kasancewar rana daya aka kawo ni da ita.
 

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN