Legit Hausa
An zabi gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, a matsayin
shugaban Kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC Legit.ng ta rahoto cewa kungiyar ta
bayyana haka ne a shafinta na tweeter a ranar Juma’a, 24 ga watan Mayu.
An tattaro cewa an zabi Bagudu ne a taron gwamnoni da aka
gudanar a Abuja a daren ranar Alhamis, 23 ga watan Mayu, a masaukin gwamna.
Bagudu, wanda aka hada kai aka zabe shi, zai maye gurbin Gwamnan jihar Imo,
Rochas Okorocha wanda mulkinsa zai kare a ranar 29 ga watan Mayu.
A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa an zabi
Gwamna Kayode Fayemi, wanda ya kasance tsohon ministan albarkatun kasa a
matsayin shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya a lokacin taron kungiyar a Abuja.
An rahoto cewa gwamnan jihar Ekiti ya yi nasara a matsayin
wanda aka fi so ya gudanar da harkokin kungiyar bayan gwamnonin sun ki amincewa
da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Tags:
LABARI