Legit Hausa
Gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong ya zama shugaban kungiyar
gwamnonin arewa na wasu shekaru hudu masu zuwa. Takwarorinsa ne suka zabe shi a
lokacin taron kungiyar gwamnonin arewa wanda ya gudana a Kaduna a ranar Juma’a,
17 ga watan Mayu.
A wajen taron wanda shine na farko a shekarar nan, gwamnonin
sun amince da kafa wani hukumar kudi na hadin gwiwa wanda zai taimaka wajen
kawo ci gaban al’umma da tattalin arziki a yankin sannan hakan zai bayar da
damar dogaro da kai ta bangaren kudi.
Gwamnonin sun kuma yanke shawarar ganawa da shugaban kasa
Muhammadu Buhari kan matsalolin tsaro a yankin.Ana sanya ran ganawar gwamnonin
wanda daga bisani ya shiga sirri, zai samu jawabai akan yanayin tsaro a fadin
jihohin da kuma sadaukarwa daga jami’an kamfanin ci gaban arewacin Najeriya kan
nasarorin da aka samu a fannin hako mai a tafkin Chadi, da kuma farfado da
durkusashen kamfanin buga kayayyaki na Kaduna mallakar jihohin arewa 19.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi