Legit Hausa
Wasu gungun fusatattun yan acaba sun yi zuga zuwa ofishin
yansandan Najeriya dake garin Zuba na jahar Neja, inda suka banka ma ofishin
wuta tare da kona motocin da yansandan suke amfani dasu wajen gudanar da
sintiri.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan acaban sun dauki wannan
mataki ne bayan cin zarafin guda daga cikinsu da Yansandan suka yi saboda yaki
amincewa ya basu kudi, inda yan acaban suka ce sun gaji da cin zalinsu da
Yansandan suke yi suna kwace musu kudi.
Wannan lamari dai ya auku ne da misalin karfe 8 na safe zuwa
karfe 10 na safiyar Alhamis, 23 ga watan Mayu, wanda hakan ya janyo zaman dar
dar da tashin hankali a yankin, tare da gurgunta hada hadar kasuwanci don
tsoron abinda kaje ka dawo.
Wani dan Achaba dake yankin yace “Yansanda sun sha tare yan
acaba suna kwace mana kudi, sun mayar damu tamkar na’urar ATM da take basu kudi
a duk lokacin da suka ga dama, don haka muka dauki alwashin ba zamu lamunci
wannan cin zali ba, sai dai su kashemu,” Shima kaakakin Yansandan babban birnin
tarayya Abuja.
DSP Anjuguri Manzah ya tabbatar da kai harin tare da kona
ofishin Yansandan, inda yace tuni sun kaddamar da bincike akan lamarin, tare da
burin kama duk masu hannu a ciki.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi