Legit Hausa
Yan bindiga sun kai mumunan hari
gidan tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa inda suka kashe mutum
guda, kuma sukayi garkuwa dan danuwansa awa 12 bayan yayi raddi kan yan ta'adda
Wannan harin yazo ne a kalla sa'o'i 24 bayan tsohon gwanman ya kaddamar da
gidauniyarshi a Abuja wacce yake niyyar amfani da ita domin taimakawa wajen
magance matsalolin taaddanci da garkuwa da mutane musamman a arewacin Najeria.
Yan ta'addan kuma sunyi garkuwa da
dan danuwanshi mai kimanin shekaru 16 mai suna Abdurrasheed Saidu wanda yake a
gidan a lokacin. Yayinda yake tabbatar da harin da aka kai, babban jamiin
gidauniyar Dr. Sulaiman Shuaibu Shinkafi yace an kai harin da misalin karfe 9
na marece a ranar jumaa.
Shinkafi ya kara da cewa maharan,
wanda sunkai kimanin mutum 60 dauke da bindiga kirar Ak 47 sunzo ne akan babura
kuma sun sayi mai na naira 5000 a garin kafin kai harin a gidan. Da aka tuntubi
mai magana da yawun yansanda na jihar Sokoto DSP muhammad Sadiq yace bashi da
masaniya game da wannan harin.
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi