Yadda wani magidanci ya yi wa matarsa dukan ajali domin ta hana shi jima'i

Ba ainihin hoton lamarin bane
Yansanda a birnin Lagos sun gurfanar da wani magidanci mai shekara 31 mai suna Godspower Johnson bisa tuhumar kashe matarsa bayan ya yi mata duka domin ta hana shi jima'i.

Mai gabatar da kara na yansanda Safeto Oladele Adebayo ya gaya wa Kotun Majistare na Ebute-Meta cewa wanda ake tuhumar ya aikata laifin ne ranar 21 ga watan Maris da karfe 5:30 na yamma a gidansu da ke lamba 28 Adekoye street, Igbo-Elerin, a Ishashi.

Safeto ya ce "Ranar da lamarin ya faru, Johnson ya yi kokarin ya sadu da iyalinsa, amma sai ya sa yatsuntsa biyu a al'aurarta, amma bata so hakan ba,  sai rigima ya kaure kuma daga bisani ta fasa yin jima'in. Wannan lamari ya fusata Johnson kuma ya rufe matarsa da duka. Daga bisani kuma ta mutu sakamakon raunuka da ta samu domin dukan da John ya yi mata".

Alkalin Kotun Chief Magistrate, O.O. Olatunji ya tasa keyar John zuwa Kurkuku har tsawon kwana 30 nan gaba yayin da ake jiran shawara daga ofishin DPP na jihar Lagos kan lamarin.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN