Yadda aka gano gawar wata daliba har ta fara rubewa a dakin kwanan dalibai na jami;ar Jos


Legit Hausa

An samu gawar wata daliba, Mercy Naan, mai shekaru 23, dake shekara ta biyu a bangaren karatun kasuwanci, a dakin kwanan dalibai mai suna 'Zion' a Naraguta. Tun a ranar 3 ga watan Mayu, iyayen dalibar suka shigar da korafi a ofishin tsaro na jami'ar a kan cewar diyar su ta bata.

Rundunar 'yan sandan jihar Filato, ta bakin kakakinta, DSP Tyopev Terna, ta tabbatar da labarin mutuwar dalibar, ta ce an gano gawar ta ne bayan daliban dake kwana a dakin sun yi korafi da wani wari mai karfin gaske dake fitowa daga dakin dalibar ranar Lahadi.

Rundunar 'yan sandan ta ce liktoci a asibitin jami'ar sun tabbatar da mutuwar ta, sannan an ajiye gawar a dakin ajiya na sashen karatun ilimin sanin sassan jikin bil'adama (Anatomy). Kazalika ta bayyana cewar ta fara binciken sarkakiyar dake tattare da mutuwar matashiyar dalibar.

Sai dai, da aka tuntubi mataimakin rijistaran jami'ar mai kula da bangaren yada labarai da sadarwa, Abdullahi Abdullahi, ya ce jami'ar na gudanar da bincike domin tabbatar da cewar matashiyar dalibar makarantar ce ta hakika Abdullahi ya kara da cewa da zarar hukumar jami'ar ta kammala bincike tare da samu dukkan bayanan marigayiyar, za a tuntubu iyayenta kafin jami'ar ta fitar da wani jawabi a hukumance.

Ya bayyana cewar matukar ba hakan jami'ar tayi ba, duk wani jawabi za ta dauke shi ne a matsayin hasashe kawai, ya kara da cewa hukumar makarantar da hadin gwuiwar hukumomin tsaro za su gudanar da binciken kwakwaf a kan lamarin

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN