Legit Hausa
A yau Alhamis dinnan ne 2 ga watan
Mayu, 2019, jirgin saman yakin kasar Isra'ila ya kai wani mummunan hari kan
dakarun Hamas a arewacin Gaza.
Sojojin Isra'ilan sun bayyana cewa
sun kai harin ne bayan da wata wuta ta kama a daji kusa da Eshkol da ke yankin kudancin
Isra'ila. Rahotanni sun nuna cewa wutar ta kama ne saboda wani abun fashewa da
ya fashe a kusa da wani birni na kasar Isra'ila.
Wasu shaidu 'yan kasar Palasdinu sun bayyanawa
kamfanin dillancin labarai cewa jirgin saman ya kai harin kan wani yanki na
sansanin sojojin Hamas a arewacin Gaza. Rahotanni sun nuna cewa, ba ayi asarar
rai ba, amma an bata abubuwa da dama a sansanin sojojin.
"Sojojin Isra'ila za su cigaba
da kashe duk wasu mutane da suka yi yunkurin cutar da al'ummar kasar
Isra'ila," in ji rahoton. An kwashe shekaru masu yawan gaske ana samun
hare-hare a yankin zirin Gaza.
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi