Legit Hausa
A yayin da kabilun jahar Taraba da na jahar Benuwe ke cigaba
da baiwa hammata iska wanda hakan yayi sanadiyyar asarar rayuka da dimbin
dukiya a tsakaninsu, shi kuwa gwamnan jahar Taraba, Darius Ishaku ba wannan
matsalar bace a gabansa.
Legit.ng ta ruwaito gwamnan jahar Taraba, Darius Ishaku ya
haramta amfani da bakar leda a jahar Taraba kwata, kai bama bakar leda ba,
kowanne irin ledar amfani yau da kullum da duk wata jakar da aka sarrafata da
roba Darius Ishaku ya bayyana cewa yayi wannan doka ne domin shawo kan
barazanar da ledoji ke yi ma muhalli a jahar Taraba, kamar yadda ya bayyana a
yayin kaddamar da tsarin tsaftace ruwa, tsaftace muhalli da kuma tsaftar jiki.
Gwamnan ya bada tabbacin nan bada jimawa ba zai aika da
kudurin dokar haramta amfani da leda a jahar Taraba ga majalisar dokokin jahar
domin ta samu amincewarsu ta yadda zama tabbatacciyar doka mai zaman kanta.
Haka zalika gwamnan ya bayyana godiyarsa bisa kokarin samar
da tsaftataccen ruwan sha ga al’ummar jahar da hukumar bada tallafi ta kasar Amurka,
USAID da na kasar Japan JAICA suke yi, don haka ya bukaci hukumar ruwan sha ta
jahar data tabbata ta kula da lafiyar bututun dake kai ruwa ga jama’a a jahar.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi