Wani babban jigon PDP da magoya bayansa sun sauya sheka zuwa APC


Legit Hausa

Wani dan takaran majalisan wakilai a majalisan People’s Democratic Party (PDP) a zaben kasa da ya gabata, Mista Olakunle Ojo, da magoya bayansa, sun sauya sheka daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC). Farfesa Afolabi Ojo, ya sauya sheka a Ward 11 a Ado Ekiti, a ranar juma’a, 31 ga watan Mayu.

Yace ya yanke shawaran ne, saboda tsohuwar jam’iyyarsa ta PDP ta ci amanar al’umma saboda haka bai ga amfani da cigaban da zai iya samu ba a harkarsa na siyasa da kuma na magoya bayansa. Daga cikin wadanda suka karbi bakuncinsa sun hada da mataimakin shugaban jam’iyyar APC, Hon. Sola Elesin, shugaban APC,na karamar hukumar Ado, Hon. Mike Akinleye da shugaban jam’iyyar a Ward 11, Mista Adegoke a madadin kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar wanda Hon Paul Omotosho ke shugabanta. 

Yayin da yake magana a madadin kwamitin, Elesin, yace zaben gwamna na 2022 zai zo ma jam’iyyar da sauki idan Fayemi ya kammala aiwatar da ajendansa guda hudu. Yace yana yiwuwa gwamnan yayi nasarar yin haka idan jam’iyya mai mulki ta daidaita hadin kai tsakanin mambobi. 

Shugaban APC, a karamar hukumar Ado, Mista Mike Akinleye yace wadanda suka sauya shekar za su ga gata kamar yadda ake nuna wa tsoffin mambobin jam’iyyar. Ya bukace su da su yi amanna da kwarewar gwamna Kayode Fayemi wajen inganta arzikin jihar.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN