Tsautsayi: Mota ta bi yaro mai shekara 4 har cikin gidan mahaifinsa ta murkushe shi

Wani yaro mai shekara 4 Segun Egunbambi, ya gamu da ajalinsa a cikin gidan mahaifinsa da safiyar Asabar, bayan wata mota ta fasa bangon gidan kuma ta sameshi ta murkushe shi har lahira.

Lamarin ya faru ne a unguwar Aduragbemi da ke Alagbado a birnin Lagos da safiyar Asabar yayin da yaron ke wasa a tsakar gidansu, kwatsam sai wata mota kirar Toyota Camry mai lamba KTU 242 FC wanda direbanta mai suna Adenowo Adeyiga yake tukawa bayan ya dawo daga Ijegun sai burki ya kwace masa.

Majiyarmu ta ce direban ya yi ta kokarin shawo kan motar, amma tsautsayi da ajali ya yi kira a lokaci daya sai motar ta shige gidan kuma ta tafi kai tsaye ta murkushe yaron.
 
DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN