Legit Hausa
Wasu kungiyoyi biyu dake rajin
tabbatar da mulki nagari a Najeriya, CD da CACOL sun ce matukar gwamnatin
tarayya ta bar harkokin tsaro a yankin arewa maso yamma suka cigaba da
tabarbarewa, babu shakka nan ba da dadewa ba 'yan bindiga zasu kai wa shugaban
kasa Muhammadu Buhari hari ko kuma ma su sace shi.
Kungiyoyin biyu sun bayyana hakan ne
a wata hira daban-daban da jaridar Punch tayi da su. Shugaban kungiyar CD na
kasa, Usman Abdul, ya ce, "bari na fada muku, da a ce shugaba Buhari ya na
garin Daura ranar da 'yan bindiga suka kai hari, zasu iya sace shi.
"Daga cikin alkawuran da
shugaban kasa ya yi lokacin yakin neman zabe akwai batun inganta tsaro a fadin
kasa. Amma abin takaici, yanzu haka maganar nan da muke yi, surukin shugaban
kasa yana hannun masu garkuwa da mutane, ita kuma fadar shugaban kasa ta shiga
juyayin sace shi. "Abin kunya ne a ce gwamnati ta gaza samar da tsaro ga
'yan kasa, wanda yin hakan shine dalili na farko da yasa aka kirkiri gwamnati.
Kalaman Garba Shehu, kakakin
shugaban kasa sun tabbatar mana cewar gwamnati ta gaza a bangaren tsaron
lafiyar 'yan kasa da dukiyoyin su." A nasa bangaren, babban darektan
kungiyar CACOL, Debo Adeniran, ya ce, "rashin kwarewa wajen iya tattara
bayanan sirri ne ya jawo aka kai hari Daura.
Da a ce jami'an tsaro sun bi hanyar
da ta dace wajen samun bayanan sirri, da hakan ba ta faru ba. "Abinda na
yarda da shine; 'yan bindigar na son tabbatar wa da duniya cewar da suna son
kai wa shugaban kasa hari, da sun yi hakan. Shugaban kasa kan ziyarci garin
Daura lokacin sallah da sauran su. Sakon da 'yan bindigar suka aika shine babu
wanda ya tsira daga sharrin su. Akwai bukatar jami'an tsaro su canja dabarunsu
na yaki da aiyukan ta'addanci."
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi