Legit Hausa
A yau mun kawo maku takaitaccen tarihin rayuwar ‘Dan takarar
jam’iyyar PDP na Gwamna a Zamfara a zaben da ya gabata watau Dr. Bello
Mutawalle wanda ke shirin karbar mulkin jihar a makon nan.
1.
Haihuwa Bello Matawalle zai shiga cikin sahun
Gwamnoni masu kananan shekaru a Ranar Laraba idan aka rantsar da shi. An haifi
Matawalle ne a Disamban 1949 a cikin Garin Muradun. A karshen shekarar nan ne
zai cika shekara 50 a Duniya.
2. Karatu Matawallen Muradun ya soma karatunsa ne a gida
watau cikin karamar hukumar Muradun inda yayi firamare ya kare a 1979. Bello
Matawalle yayi karatu a kwalejin fasaha ta Yaba da ke Legas sannan kuma ya tafi
wata Jami’a a Landan.
3. Aikin Gwamnati Mai shirin zama Gwamnan na Zamfara yayi
aikin malanta a makarantun gwamnatin jihar Sokoto da ke Garin Moriki da
Kwatarkwashi a karkashin ma’aikatar lafiya. Daga baya kuma ya koma Ma’aikatar
harkar ruwa ta tarayya.
4. Siyasa A 1998 ne Mutawallen Muradun ya shiga harkar
siyasa, ya zama ‘dan jam’iyyar UNCP. Bayan kafa gwamnatin ANPP a Zamfara ne ya
zama Kwamishinan harkar kananan hukumomi, daga baya kuma aka nada sa Kwamishina
na Matasa.
5. Takara A 2003 Mutawallen Muradun ya nemi takarar kujerar
majalisar tarayya mai wakiltar Muradun da Bakura. Wannan ya sa ya bar gwamnatin
Ahmad Yariman-Bakura. Mutawalle ya tafi majalisar har sau 3 inda ya bar
kujerarsa a 2015.
6. Sauya-sheka Bello Matawalle ya bar jam’iyyar ANPP ne ya
koma PDP a 2009 lokacin da aka samu sauyin-siyasa a jihar Zamfara. A karkahsin
jam’iyyar PDP ne Matawalle ya sake samu ya koma majalisa a zaben 2011 wanda ya
zama karon karshe.
7. Gwamnan Zamfara A 2019 ne Bello Matawalle ya tsaya
takarar Gwamna inda yayi alkawarin maida hankali a kan harkar ilmi da kiwon
lafiya da sha’anin tsaro idan ya samu mulki. Ko da ya fadi zabe, kotu ta ba sa
nasara bayan kuri’un APC sun tashi a tutar babu.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi