Legit Hausa
Hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC a ranar Talata ta karbe
shahadar da ta baiwa biyu daga cikin sabbin yan majalisar dokokin jihar Kaduna.
Wadannan yan majilasar dai sune, Haruna Aliyu wanda aka fi sani da Chakis sai
kuma Ibrahim Ismail.
Haruna Aliyu yana wakiltar Kaduna ta Arewa 2 (Kawo) yayin da
shi kuma Ismail Ibrahim yana wakiltar Kaduna ta Kudu 2 (Tudun Wada). Wadannan
mutane biyu sun fafata a zaben fitar da gwani karkashin jam’iyar APC a watan
Oktoban 2018.
Inda abokan karawarsu su kayi nasara akan su, Yusuf Salihu
mai kuri’a 104 shine ya doke Haruna Aliyu a zaben yayin da shi kuma Ibrahim
Ismail ya sha kashi a hannun Nasiru Usman wanda ya samu kuri’a 49. Jam’iyar APC
bata kai sunayen wadanda suka lashe zaben fidda gwanin ba sai ta kai sunayen
Haruna Aliyu wanda ya samu kuri’a 24 da kuma Ibrahim Ismail mai 35 a matsayin
yan takarar kujerar majalisar jiha a gundumominsu.
Babbar kotun kasa dake jihar Kaduna karkashin jagoranci,
Alkali Z. B Abubakar ta yanke hukuncin cewa Nasiru Usman da kuma Yusuf Salihu
kasancewar sune mutane biyu da sukayi nasara a zaben fidda gwani na jam’iyar
APC, su ya fi dacewa da su tsaya takara.
A don haka kotun ta musanya Haruna Aliyu da Yusuf Salihu
yayin da shi kuma Nasiru Usman ya canji Ibrahim Ismail a matsayin yan majalisu masu
wakiltar Kaduna ta Arewa (Kawo) da kuma Kaduna ta Kudu (Tudun Wada). Kuma tuni
INEC ta karbe takardar shaidar ta baiwa wadanda kotu tayi umarni a bawa.
DAGA ISYAKU.COM Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi