Shin ko me ya hana tsoffin shugabannin Najeriya zuwa wajen rantsar da Buhari?


Legit Hausa

Abubuwa da dama sun auku yayin rantsar da shugaba Muhammdu Buhari a karo na biyu a sararin Eagle square dake Abuja. Abu na farko dai wanda zai matukar baka mamaki shi ne, idan ka cire Yakubu Gowon babu daya daga cikin tsoffin shugabannin kasar dake raye da ya halarci bikin rantsar da Buhari. 

Sai dai kuma a irin wannan ranar a shekarar 2015, kusan za a iya cewa dukkanin tsoffin shugabannin kasar nan sun halarci bikin inda tsohon shugaba Goodluck Jonathan ya mika mulki ga Buhari. Masu sharhi kan al’amuran siyasa irinsu Dakta Tukur Abdulkadir na jami’ar Kaduna sun danganta rashin halartar tsoffin shugabannin akan abubuwa guda biyu: 

Raba garin da Buhari ya yi da tsoffin shugabannin Kokarin fifita ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar demokradiya ta kasa Dakta Tukur yace, “ Ina tunanin tsohon shugaba Olusegun Obasanjo bai halarci taron ba saboda yadda dangantaka ta yi tsamari tsakaninsa da Buhari ta yadda har ana jifar juna da maganganu.” Shi kuwa shugaba Goodluck Jonathan “Zai yi wuya ya halarci taron kasancewarsa jigo a jam’iyar adawa ta PDP”, inji Dakta Tukur.

To amma Dakta Tukur ya ce yana ganin “rashin halartar tsohon shugaba Abdussalam Abubakar ba ta da nasaba da bacin dangantaka da shugaba Buhari kasancewar shi Abdussalam din yana shiga kusan wata s abgar Buhari da aka gayyace shi.

" Wani abu dake kara nuna tsamari tsakanin alakar shugaba Buhari da tsoffin shugabannin kasar shi ne a wata hira ta musamman da gidan talabijin na NTA inda Buhari ya furta cewa yana sane da manya kasar nan ba su son sa
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN