Legit Hausa
Hukumar Hizbah, shiyar jihar Kebbi, ta ceto wata jaririyar
yar kwanaki biyu da haihuwa bayan mahaifiyarta ta birneta da rai. An gano gawar
yar jaririyar kwana biyu bayan haihuwarta a bayan wani Otal dake cikin garin
Birnin Kebbi.
Mahaifiyar yarinyar da wata kawarta sun kama daki a
shahrarran Otal mai suna Zinari, na tsawon kwana biyu kuma suka silale suka
birne yarinyar cikin dare a bayan Otal. Diraktan bangaren Shari'a da harkokin
addinin jihar, Alhaji Abubakar Muhammad Lamne Augie, ya ce kukan yar jaririyar
ya jawo hankalin jama'a kuma suka cirota daga inda suka birneta.
Yace: "Mahaifyar yarinyar ta birne jaririyar da ranta
bayan sun zauna a Zinari Hotel na tsawon kwana biyu." Bayan birne
jaririyar, sai suka leka ko yarinyar ta mutu. Amma da suka hakota, sai yarinyar
ta fashe da kuka, sai suka ruga da gudu.
" Ya ce yarinyar bata daina kuka ba har sai da jama'a
suka ji kukan kuma suka ceceta. sai Jama'a cirota daga kasa, sannan suka sanar
da hukuma domin ceton rayuwar yarinyar. Kana mazauna unguwar sun shiga cikin
Otal din kuma duka damke wadannan yan mata biyu. Tsokaci: Hoton da muka sanya
na bayani ne kawai, ba ainihin hoton jaririya bane.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi