Legit Hausa
A jiya Talata 14 ga watan Mayu, 2019, kotu ta tura wani
mutumi dan shekara 40, mai suna Sani Ibrahim, gidan yari bayan ta kama shi da
laifin yiwa yarinyar makwabcinsa fyade.
Ibrahim, wanda zai kasance a gidan kurkuku har zuwa ranar 26
ga watan Yuni, 2019, kotu na tuhumar sa da aikata fyade a karkashin sashe na
283 na dokar kasa.
Wani jami'in dan sanda ya bayyanawa kotu cewa, mahaifin
yarinyar, Hamisu Lawali, shine ya kawo karar lamarin a ofishin 'yan sanda na
Bindawa, ranar 9 ga watan Mayu, kasa da sa'o'i biyu bayan an kama Ibrahim
lokacin da yake yiwa yarinyar fyade.
Ibrahim, Lawali da yarinyar da aka yiwa fyaden, duk mazauna
unguwar Sabuwa Abuja ne dake karamar hukumar Bindawa cikin jihar Katsina.
Lawali ya bayyanawa 'yan sanda cewa ba wannan ne karo na farko da Ibrahim ya
aikata laifin ba.
A bayanin da dan sandan ya bayar, ya bayyanawa Kotun
Majistire ta Katsina, cewa bayan an binciki Ibrahim, ya bayyana cewa ya kwanta
da yarinyar har sau uku. Ba wannan ne karo na farko da kotu ta ke yin hukunci
akan irin wannan lamari na fyade ba.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi