Sabon gwamnan jihar Gombe ya rusa dukkan kwangiloli da nade-naden da Dakwambo ya bayar na karshe


Legit Hausa

Jim kadan bayan ranstar da shi a matsayin sabon zababben gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yayha AbdulKadir, ya sanar da cewa ya soke dukkan nade-nade, kwangiloli, filaye da gwamna mai barin gado, Ibrahim Dankwambo, yayi daga ranar 10 ga Maris, 2019 zuwa yanzu. 

Kana sabon gwamnan ya bayyana cewa zai sake dubi kan sabbin makarantun gaba da sakandaren da gwamnatin tsohon gwamna Ibrahim Dankwambo tayi bayan nazari kan yiwuwan tafiyar da su dubi ga irin basussukan da aka bari na sama da N110 biliyan. 

Ya yiwa alkawarin magance matsalolin da ya dukufar da ma'aikatun gwamnatin jihar ta hanyar dubi cikin jin dadin ma'aikata, karin girma da alawus. Inuwa Yahya ya kara da cewa zai gudanar da gwamnatinsa ta hanyar bude kofa ga kowa ya kawo korafe-korafe ko shawari masu kyau. 

Hakazalika ya umurci dukkan sakatarorin kanana hukumomi 11 su dau ragamar mulkin kananan hukumominsu kafin nada sabbin shugabannin rikon kwarya ko zaben shugabanninsu. Amma, gwamna mai barin gado, Ibrahim Dankwambo, bai halarci wannan taron rantsarwa ba kuma ba'a bada wani bayani kan haka ba. 

Mun kawo muku rahoton cewa An baza jami’an tsaro a ciki da wajen babban filin wasan Pantami a Gombe a ranar Laraba, 29 ga watan Mayu, yayin da ake gudanar da bikin rantsar da Inuwa Yahaya a matsayin zababben gwamnan karo na hudu a mulkin damukardiyya a jihar Gombe.
 

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN