• Labaran yau


  Sabbin Sarakuna: Mahaifin sanata Kwankwaso ya yi biyayya ga umarnin Ganduje


  Legit Hausa

  Musa Kwankwaso, hakimin karamar hukumar Madobi kuma mahifi ga tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ya janye biyayyar sa ga sarkin Kano Muhammadu Sanusi II. A cikin satin da ya gabata ne gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya rattaba hannu a kan dokar masarauta da majalisar dokokin jihar tayi wa garambawul. 

  Daga cikin gyaran da aka yiwa dokar akwai bukatar kara kirkirar sabbin masarautu hudu da sarakuna masu daraja daya da ta sarkin Kano. Sabbin masarautun da dokar ta amince da kirkirar su akwai, Bichi, Gaya, Karaye da Rano. Sabbin Sarakuna: Mahaifin sanata Kwankwaso ya yi biyayya ga umarnin Ganduje A ranar Asabar ne gwamna Ganduje ya rantsar da sabbin sarakunan masarautun tare da basu sandar iko, sannan ya umarci duukan masu rike da sarautar gargajiya da malaman addini da suyi mubaya'a ga sabbin sarakunan yankin da suka tsinci kan su.

  Sabanin wasu masu rike da sarauta da suka yi murabus ko kin yin biyayya ga sabbin sarakunan, Musa Kwankwaso ya jagoranci kafatanin masu rike da sarauta dake karkashin sa wajen kai ziyarar yin muba'a da biyayya ga sabon sarkin Karaye, Ibrahim Abubakar II, da masarautar karamar hukumar Madobi ta koma karkashin ikon sa. Wannan ziyara ta Musa Kwankwaso ta nuna cewar ya yi biyayya ga umarnin Ganduje, ya janye biyayyar sa daga tsohuwar masarautar Kano.
   

  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Sabbin Sarakuna: Mahaifin sanata Kwankwaso ya yi biyayya ga umarnin Ganduje Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama