Legit Hausa
An sanar da mutuwar Dakta Ibrahim Yakubu Lame, jigo kuma dan
takarar gwamnan jihar Bauchi a karkashin inuwar jam'iyyar APC a zaben shekarar
2019 da aka kammala.
Lame ya taba rike mukamin minista mai kula da harkokin
rundunar 'yan sanda, sannan yana rike da sarautar 'Santurakin Bauchi'. Dan
siyasar ya rasu ne da samyin safiyar yau, Lahadi, a asibitin Nizamiye dake
Abuja bayan ya sha fama da rashin lafiya.
An sallaci gawar sa da misalin karfe 10:00 a babban
masallacin kasa dake Abuja, birnin tarayya. Wani mai nazari a kan harkokin
jama'a daga jihar Bauchi, Musa Azare, ya bayyana mutuwar a matsayin babban
rashi ga kasa.
An haifi Marigayi Lame, malami kuma dan siyasa, a shekarar
1953, sannan an zabe shi a matsayin sanata a shekarar 1992 lokacin jamhuriya ta
uku. Toshon shugaban kasa Obasanjo ya nada shi a matsayin mai bashi shawara a
shekarar 1999 kafin daga bisani tsohon shugaban kasa, Marigayi Umaru Musa
Yar'adua, ya nada shi minista a shekarar 2008.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Tags:
LABARI