Legit Hausa
Kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa, NSGF ta kafa wata
gidauniyar kudi a kan Naira biliyan shida domin farfado da tattalin arzikin
yankin da kuma kawo cigaba. Shugaban kungiyar mai barin gado, gwamna Kashim
Shettima na jihar Borno ne ya bayar da wannan sanarwar yayin da ya ke bitan
nasarorin da ya samu a shekaru hudu da suka gabata a ranar Juma'a a Kaduna.
Ya ce an dauki wannan matakin ne domin tabbatar da cewa
yankin arewa ya fara dogoro da kansa a fanin samar da kudade. Ya ce a karkashin
shirin za a farfado da masakun yankin da kuma kamfanin New Nigeria Development
Company (NDDC).
Shettima ya ce ana sa ran gwamnonin jihohin arewa 19 ne za
su tattaro kudin da za kamfanin za tayi amfani dashi. A halin yanzu sun tara
Naira miliya 650. "Domin cimma burin mu, ko wace jiha za ta rika bayar da
gudunmuwar Naira miliyan 50 kowane wata na tsawon watanni shida.
"A halin yanzu, muna da N560 miliyan a cikin N5.7
biliyan da muke bukata. Ina kira ga jihohin da ba su cika alkawurransu ba da
suyi kokarin yin hakan domin su samu damar fara ayyukan da muka tsara a
karkashin shirin.
"Ayyukan sun hada da samar da kamfanin lantarki da zai
iya samar da wuta mega watt 3000 zuwa 4000. "Kungiyar kuma ta fara daukan
matakan farfado da kamfanin New Nigeria Development Company, NDDC don ya cigaba
da aikinsa a matsayin cibiyar kasuwanci da tattalin arziki na yankin
arewa," inji shi.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Tags:
LABARI