Legit Hausa
Ku na da labari cewa a kwanakin baya ne jami’an tsaro na DSS
su ka damke wani Malamin addinin Musulunci mai suna wani Malamai mai suna Aminu
Usman watau Abu Ammar a jihar Katsina. An tsare wannan babban Malami ne bayan
ya koka a kan yadda sha’anin tsaro ya tabarbare a jihar Katsina.
Malamin ya bayyana cewa shi kadai ya ga irin abubuwan da ya
gani a lokacin da ya ke hannun Jami’an DSS na kasar. Malamin yake cewa ba
wannan ne karon farko da aka kama shi ba, ya kuma ce wannan abu bai sa ya
karaya ba. Ustaz Abu Ammar ya godewa irin addu’o’in da jama’a su ka rika yi
masa inda yace wannan ne ya sa ya samu kubuta.
Wannan Malami ya fadawa ‘Dalibansa cewa wasu ne su ka shirya
masa tuggu a wajen jami’an tsaro, ko da yake dai Malamin ya ki bayyanawa
Almajiran na sa irin yadda ya sha ta-ta-burza da jami’an tsaron na DSS masu
fararen kaya.
Abu Ammar yake cewa babu abin da zai ga bayan da’awar yadda
Sunnah a Katsina da Najeriya ko da jami’an tsaro sun cafke sa. Malamin ya nemi
jama’a su tsayawa gaskiya a kowane lokaci ba tare da goyon bayan wani mutum
ba.Shehin yake cewa dole yayi magana a kan irin kashe-kashen rayukan mutanen da
ake yi a Garuruwan Batsari, Danmusa, Kankara, Sabuwa, Dandume, Faskari, Jibiya,
K atsina, Mani, Daura da Batagarawa, har da kuma cikin Garin Katsina.
Malamin addinin musuluncin ya kuma nuna babu hannun
gwamnatin jihar Katsina ko ta tarayya wajen daure sa da aka yi. Malam Abu Ammar
yake cewa wasu ne su ka sa aka cafke sa inda yayi mumunan addu’a ga masu
nemansa da sharri. A jawabin Malamin lokacin da ya koma karatun tafsiri a makon
jiya, yace babban burinsa shi ne a kawo karshen kashe-kashen mutanen da ake yi
a Katsina kamar yadda ya bayyana a wata hudubar sa.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi