Legit Hausa
A ranar Laraba, 15 ga watan Mayu, ne wata babbar kotun jihar
Kano a karkashin mai shari'a, Jastis Nasiru Saminu, dake zamanta a yankin
karamar hukumar Ungoggo ta bayyana sabbin masarautu hudu da gwamnan jihar Kano,
Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya kirkira a matsayin haramtattu.
Kotun ta bayar da bayar da umarnin rushe sarakunan tare da
koma wa karkashin tsarin da ake kai a baya har sai an kammala sauraren karar da
aka shigar a kan nadin sabbin sarakunan. A ranar Asabar ne gwamna Ganduje ya
nada sabbin sarakunan yanka hudu a jihar Kano biyo bayan amincewa da dokar
kirkirar sabbin masarautu da majalisar dokokin jihar Kano tayi.
Tun a ranar Juma'a, kwana daya kafin bikin nadin sabbin
sarakunan, wata kotun jihar Kano ta bukaci gwamna Ganduje ya dakatar da gudanar
da bikin nadin sabbin sarakan. Amma sai gwamnatin jihar ta bayyana cewar
umarnin ya zo mata ne bayan ta rika bawa sabbin sarakunan takardar nada su.
Ana zargin Ganduje da kirkirar sabbin masarautun domin
daukan fansar siyasa a kan sarkin Kano Muhammadu Sanusi II domin rage masa
karfi da ikon da yake da shi. Amma gwamnan ya kafe kan cewar babu wata matsala
tsakaninsa da sarkin, tare da bayyana cewar ya yi hakan ne domin kishin jihar
Kano da cigaban ta.
Wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a nadin sarkin Kano da
suka hada da - Madakin Kano, hakimin Dawakin Tofa, Yusuf Nabahani; Makaman
Kano, hakimin Wudil, Abdullahi Sarki Ibrahim; Sarkin Dawaki Mai Tuta, hakimin
Gabasawa, Bello Abubakar da Sarkin Ban Kano, hakimin Dambatta, Mukhtar Adnan,
sun kara shigar da karar gwamna Ganduje da gwamnatin jihar Kano.
Majalisar dokokin jihar Kano, kwamishinan shari'a na jihar
da sabbin sarakunan da aka nada - Tafida Abubakar Ila, Ibrahim Abdulkadir,
Ibrahim Abubakar II da Aminu Ado Bayero - na daga cikin mutanen da aka shigar da
karar.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi