Legit Hausa
Sabanin shahararren hasashen nan da ke yawo, bincike da
hujjoji da suka billo sun nuna cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba yankin
kudu manyan mukamai masu maiko a kasar fiye da yanda yayi a arewa.
Takardu da ke kunshe da nade-naden da Shugaban kasa Buhari
yayi a gwamnatinsa na farko a 2015 ya nuna cewa akwai daidaito tsakanin
yankunan biyu, jaridar Vanguard ta ruwaito. Misali, jihar Ogun ce a saman jarin
mukaman inda take da nade-nade 31, fiye da nade-naden da jihohin arewa maso
yamma uku ke dashi wanda suka hada da Kebbi 13, Zamfara bakwai da kuma Sokoto
mai shida.
A arewa maso yamma, jihar Katsina ce da mukamai mafi yawa
guda 24, yayinda Kaduna da Kano suka samu 16; inda Jigawa ke da 12. Inda a
nade-naden siyasa kudu maso gabas ce keda mafi karanci, Imo ce ta uku a nadin
MDA (nade-nade 29), sannan aka bai wa Anambra 20 inda Abia ta samu 14.
Jihohi kamar su Enugu da Ebonyi na da takwas da bakwai. Sai
dai kuma, takardu dun nuna cewa yawan nade-naden shugabanni a ma’aikatu, kaso
51 cikin dari ya tafi ne ga jihohin arewa 19, sannan kaso 49 cikin dari ya tafi
ga jihohin kudu 17.
A daya bangaren, manyan nade-naden siyasa 124 kamar irin su
masu bayar da shawara na musamman, manyan masu bayar da shawara, da kuma
hadimai na musamman ga Shugaban kasa sun kasance 59 daga arewa sannan 65 daga
kudu.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi