Legit Hausa
Tsohon Shugaban masu rinjaye a
majalisar dattawa, Ali Ndume, ya nuna karfin gwiwar cewa zai zamo Shugaban
majalisar dattawa ta tara, a wata mai zuwa.
Koda dai jam’iyyar All Progressives
Congress (APC) mai mulki ta nuna Sanata Ahmad Lawan ne zabinta a wannan kujera,
Ndume ya dogara da goyon bayan takwarorinsa da shugabannin jam’iyyar.
Da yake jawabi ga manema labarai a
Lagas, a jiya Litinin, 6 ga watan Mayu, Ndume, wanda yace bai shiga tseren
domin yin cinikin kowani mukami mai gwabi-gwabi ba, ya jadadda cewa ya tuntubi
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, babban jigon APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu
da sauran shugabannin jam’iyya mai mulki, akan kudirisa, sannan kuma cewa
dukkansu sun sanya masa albarka a kudirinsa.
Ndume ya ci gaba da bayyana cewa,
babu wanda ya nemi ya janye ma wani daga tseren. Tsohon Shugaban masu rinjaye a
majalisan yace hatta da Shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole, yayi bayanin
cewa jam’iyyar dai ta gabatar da Sanata Lawan ne a matsayin dan takarar da tafi
so sannan ba wai tana kokarin tursasa shi akan sanatoci bane.
Da yake Magana akan ajandarsa, Ndume
wanda a yanzu yake wakiltan Borno ta kudu, yayi alkawarin inganta kokarin da
majalisa ta takwas tayi, sannan ya kara da cewa zai rage kwadaitar da mukamin
Shugaban majalisar dattawa ga mutane ta hanyar rage wasu abubuwa marasa amfani
da ke jingine da kujerar.
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi