Ministan Shari'a na Najeriya Abubakar Malami ya yi murabus


Legit Hausa

Lauyan koli kuma Ministan Shari'a na kasa, Abubakar Malami, ya ce kawowa yanzu kudaden da ma'aikatar sa ta kwakulowa gwamnatin tarayya sun kai kimanin Naira biliyan 270 daga kan Naira biliyan 19.5 da su ke a shekarar 2015. 

Malami wanda ya kasance zababben Ministan shugaban kasa Muhammadu Buhari daga jihar Kebbi, ya bayyana hakan ne cikin garin Abuja yayin gabatar da jawaban sa na bankwana na kawo karshen wa'adin sa a matsayin jagoran ma'aikatar shari'a ta kasar nan. 

A cewar wani rahoto daga jaridar Vanguard ta fitar, Malami ya ce gwamnati ta shirya tsaf wajen tabbatar da dawowar kadarorin ta da suka kai kimanin dalar Amurka miliyan 500 daga kasar Faransa, Amurka, Jersey. 

Ya yi waiwaiye da Hausawa ke cewa adon tafiya na hobbasan sa yayin dawowa da kasar nan tarin dukiya daga kasar Switzerland ta kimanin Naira miliyan 322.5 da tsohon shugaban kasa Marigayi Janar Sani Abacha ya wawushe. 

Malami da ya kasance Ministan shari'a na kasar nan a shekarar 2015 bayan ya karba daga hannun Magajin sa, Muhammad Adoke, ya hikaito kwazon da ma'aikatar sa ta yi cikin tsawon shekaru hudu da suka gabata. 

Shakka babu masu sharhi sun shaida cewa hukumar shari'a da ta kasance a karkashin kulawar Malami, ta yi aiki tukuru wajen ba wa gwamnatin tarayya goyon bayan tare da taka muhimmiyar rawar gani a fagen yakin ta na cin hanci da rashawa.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN