• Labaran yau


  Milyan N2.5m na karba cikin N30m kudin fansan surukar gwamna Masari - Mai garkuwa da mutane


  Legit Hausa

  Kasurgumin mai garkuwa da mutane da ya jagoranci garkuwa da surukar gwamnan jihar Katsina, Hajiya Hauwa Yusuf, ya bayyana yadda ya karbi milyan biyu da rabi cikin milyan talatin da suka karba matsayin kudin fansa. 

  Dan barandan mai suna, Abubakar M. Sani alias Kubi, mazauni unguwar Sokoto Rima ya ce bayan garkuwa da dattijuwar, sun sayar da ita ga wani kungiyar masu garkuwa da mutanen da ke dajin Batsari. A cewarsa: "Ban taba saninta ba. 

  Na biyo ta unguwan ne kawai na ga a a raba takardun siyasa. Lokacin da muke saceta, daga daya cikin abokanmu yace ya san wasu yan barandan a cikin daji kuma muka mikata garesu." "Daga cikin N30m da aka biya kudin fansa, na samu N2.5m, yayinda sauran abokaina biyu suka samu milyan biyu-biyu." Kwamishanan yan sandan jihar, Sanusi, ya bayyana cewa Abubakar Dani alias Dan Bose, Rabe Hamza alias Tankabaje, Marwana Gide, Abdulhakim Bishir, ne suka sace tsohuwar. 

  Mun kawo muku rahoton cewa Hukumar yan sandan Najeriya ta samu nasarar damke wasu masu garkuwa da mutane 13 da suka addabi jihar Katsina wanda ya kai ga sace surukar gwamnan jihar, Aminu Bello Masari a ranar 8 ga watan Fabrairu, 2019. Kwamishanan yan sandan jihar Katsina, ya bayyanasu ga manema labarai a yau Litinin, 20 ga watan Mayu, 2019. 


  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Milyan N2.5m na karba cikin N30m kudin fansan surukar gwamna Masari - Mai garkuwa da mutane Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama