Messi ya fashe da kuka sakamakon duka da Barcelona ta sha a hannun Liverpool 4-0

Fitaccen dan kwallon kafa  Lionel Messi ya fashe da kuka bayan kungiyar kwallon kafa da yake wasa Barcelona ta sha kashi a hannun Liverpool da ci 4-0 mai ban haushi.

Rahotanni sun ce Messi ya gaza hakuri da jure wannan kashi da kungiyarsa ta sha a hannun Liverpool, sakamakon haka ya fashe da kuka a cikin dakin canja tufafi na yan wasan Barcalona a Anfield.

Duk da yake kungiyarsa ta ci 3-0 a karawar farko a Camp Nou. Hakazalika rahotanni sun ce bayan Messi ya isa filin saukar jiragen sama, wasu fusatattun magoya bayan Barcelona sun fuskance shi da kalamai masu zafi sakamakon gazawar nassarar Barcelona a gasar wasan zakaru.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post