• Labaran yau


  Mayakan Boko Haram sun kai hari Askira-Uba, sun yi awon gaba da kayan abinci mai yawa

  Mayakan kungiyar Boko Haram sun kai garin Lassa dake karkashin karamar hukumar Askira-Uba a jihar Borno tare da kone gidaje da shaguna da kuma yin awon gaba da kayan abinci mai yawan gaske da sauran kayan amfani. Wata majiya mai tushe, da harin ya shafi 'yan uwan ta, ta shaida wa jaridar Daily Trust a Maiduguri cewar mayakan sun kai hari garin ne da misalin karfe 8:10 na daren ranar Asabar, inda suka yi harbin iska kafin daga bisani su fara kone gidaje da shagunan mutane. Garin Lassa ya yi suna wajen harkar noma da kasuwancin kayan abinci. Majiyar ta bayyana cewar mayakar sun fi karfin dakarun sojin dake garin na Lassa a yayin da suka so dakatar da su, amma daga baya bayan karin dakarun soji sun zo daga Askira-Uba, sojojin sun kori mayakan kafin karfe 12:00 na dare. Kazalika ta bayyana cewar ba ta da masaniyar ko an samu asarar rai sakamakon kai harin, tare da fadin cewar mayakan sun kai harin ne domin su kwashi kayan abinci da ragowar kayan amfani. Read more: https://hausa.legit.ng/1239143-mayakan-boko-haram-sun-kai-hari-askira-uba-sun-yi-awon-gaba-da-kayan-abinci-mai-yawa.html


  Legit Hausa

  Mayakan kungiyar Boko Haram sun kai garin Lassa dake karkashin karamar hukumar Askira-Uba a jihar Borno tare da kone gidaje da shaguna da kuma yin awon gaba da kayan abinci mai yawan gaske da sauran kayan amfani. 

  Wata majiya mai tushe, da harin ya shafi 'yan uwan ta, ta shaida wa jaridar Daily Trust a Maiduguri cewar mayakan sun kai hari garin ne da misalin karfe 8:10 na daren ranar Asabar, inda suka yi harbin iska kafin daga bisani su fara kone gidaje da shagunan mutane.

  Garin Lassa ya yi suna wajen harkar noma da kasuwancin kayan abinci. Majiyar ta bayyana cewar mayakar sun fi karfin dakarun sojin dake garin na Lassa a yayin da suka so dakatar da su, amma daga baya bayan karin dakarun soji sun zo daga Askira-Uba, sojojin sun kori mayakan kafin karfe 12:00 na dare.
  Kazalika ta bayyana cewar ba ta da masaniyar ko an samu asarar rai sakamakon kai harin, tare da fadin cewar mayakan sun kai harin ne domin su kwashi kayan abinci da ragowar kayan amfani.


  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Mayakan Boko Haram sun kai hari Askira-Uba, sun yi awon gaba da kayan abinci mai yawa Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama