Matar shugaban kasa Aisha Buhari ta bar masa sako a shafinta na Twitter


Legit Hausa

Hajiya Aisha Buhari ta ɗaura wani bidiyo a shafin ta na Tuwita wanda ya ke ta faman jawo magana a halin yanzu. A Ranar Juma’a 24 ga Watan Mayun 2019 ne Matar shugaban kasar tayi wannan aiki. Aisha Buhari ta saka wani bidiyo ne na babban ‘dan siyasar nan na Kasar Afrika ta Kudu mai suna Julius Malema, inda yake ba sabon shugaban kasar watau Cyril Ramaphosa wasu muhimman shawarari. 

Julius Malema ya ja-kunen shugaba Cyril Ramaphosa ne a lokacin da aka rantsar da shi a kan mulki kwanaki, da ya bi a hankali da wasu manyan na-kusa da shi da ka iya kai sa su kuma baro sa. Malema ya fadawa shugaban kasar Afrikan ta Kudu cewa ka da ya biyewa ‘yan kanzagin da za su rika fada masa abin da ba gaskiya ba. 

Malema yace shugaban yana bukatar masu fada masa gaskiya a gefensa. ‘Dan siyasar ya kara da cewa akwai masu hurewa shugabanni kunne su rika fada masu sun yi daidai ko da kuwa sun yi abin da ya sabawa dokar kasa ko kuma hukuncin kotu, yace ya guji wannan mutane. 

Hajiya Aisha Buhari tayi na’am da wannan jawabi na Julius Malema inda ta sake saka bidiyon a shafin ta tana mai karin bayani da nuni da cewa ya kamata shugabanni su ka rika daukar shawarar al’umma. Matar shugaban kasar ta kuma nemi shugabanni su rika yin aiki tare. 

Hakan na zuwa ne mako guda bayan shugaba Buhari ya dawo daga Umrah tare da Iyalin na sa da kuma wasu na-hannun damansa. Jama’a su na ta faman magana a kan wannan lamari a yanzu haka ganin cewa shugaban kasar yana tare da Maman Daura da Isa Funtua har a kasar Saudi a makon jiya, wanda ake tunani su su ka zagaye sa.
 

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN