Manyan alkalai mata guda 8 da sunayen manyan 'yan siyasa da suke aure


Legit Hausa

Majiyarmu ta binciko muku jerin manyan alkalai mata guda takwas da kuma sunayen mazajen su manyan 'yan siyasa na Najeriya da suke aure Kwana biyu da suka wuce, alkalin kotun daukaka kara, Mai shari'a Zainab Bulkachuwa, ta ceto kanta daga rikicin karar zabe da take saurara, bayan da jam'iyyar PDP ta taso da zancen cewa mijinta dan jam'iyyar APC ne. 

A yau majiyarmu Legit.ng za ta kawo muku jerin manyan alkalai mata da mazajensu wadanda suke manyan 'yan siyasa ne a kasar nan. Mary Odili ita ma wata shahararriyar alkali ce, matar tsohon gwamnan jihar Rivers Dr. Peter Odili, wanda ya fito takarar shugaban kasa a lokacin mulkin PDP.
2. Zainab Bulkachuwa Zainab Bulkachuwa, ita ce shugabar kotun daukaka kara ta kasa. Tana auren zababben Sanatan APC na jihar Bauchi, Alhaji Adamu Bulkachuwa.

3. Fati Lami Abubakar Fati matar tsohon shugaban mulkin soja ne, Gen Abdulsalami Abubakar (Rtd), wanda ya hau mulki bayan mutuwar tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha a shekarar 1998.
4. Binta Nyako Binta Nyako ta na daya daga cikin many an alkalai a Najeriya wacce sunanta ya karade kowanne lungu da sako na kasar nan. Binta Nyako ita ce matar tsohon gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako, wanda yayi mulki daga shekarar 2007 zuwa 2015.

5. Eberechi Wike ita ce matar gwamnan jihar Rivers na yanzu, Cif Nyesom Wike. 

6. Maryann Anenih Maryann Anenih ita ce karama a cikin matayen Cif Anthony Anenih, tsohon shugaban jam'iyyar PDP na kasa, wanda aka fi sani da sunan shi na siyasa da Mista Fix-It. 

7. Chioma Nwosu-Iheme Dr. Chioma Nwosu-Iheme alkalin kotun daukaka kara ce. Tayi karatu a bangaren shari'a har ta kai matsayin Farfesa, kuma ita ce mace ta farko da ta fara kaiwa wannan matsayin a Najeriya. Ita ce matar tsohon kwamishinan cigaban karkara, sannan kuma kwamishinan ilimi na jihar Imo. 

8. Jumoke Pedro Jumoke Pedro ita ce alkalin babbar kotun jihar Legas, tana auren tsohon mataimakin gwamnan jihar Legas Femi Pedro.
 

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN