Majalisar Dattawa ta amince da sauya ranar Dimokuradiya a Najeriya


Legit Hausa

Majalisar Dattawan Najeriya ta yi shimfidar amanna kan kudirin amincewa da dokar ayyana ranar 12 ga watan Yuni a matsayin sabuwar ranar dimokuradiyyar kasar sabanin yadda ta kasance a baya na ranar 29 ga watan Mayu. Shimfidar aminci na majalisar na zuwa ne bayan kimanin shekara guda da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi shelar cewa za a sauya ranar Dimokuradiya ta Najeriya daga 29 ga watan Mayu zuwa 12 ga watan Yuni. 

A yayin da majalisar dattawan Najeriya yayin zaman ta na ranar Alhamis ta rattaba hannu kan wannan kudiri, majalisar wakilai ta tarayya a nata bangaren ta amince da wannan sabon kudiri tun a watan Dasumba na shekarar 2018 da ta gabata. 

A yayin zaman ta bisa jagoranci mataimakin shugaban dattawa, Sanata Ike Ekweremadu, majalisar ta yi amanna da sabon kudirin yayin da shugaban ta mai rinjaye, Sanata Ahmed Lawan ya yi fashin baki na bukatar shugaban kasa Buhari. 

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari ya sauya ranar Dimokuradiyar kasar nan domin karrama Marigayi MKO Abiola a matsayin wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 12 ga watan Yunin 1993.
 

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN