Kungiyar kwallon kafa
ta Arsenal dake kasar Ingila ta nuna sha'awar bayar da 'yan wasan ta uku
da kuma karin kudi domin daukan dan wasan gaba na kungiyar Crystal
Palace kuma dan asalin kasar Ivory Coast dake nahiyar Afrika, Wilfred
Zaha.
Zaha, mai shekaru 26, ya samu nasarar saka kwallo 10 a wasa 36 da ya
buga wa kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace a kakar wasannin bana.
A karshen watan jiya ne Zaha ya sanar da cewar yana da sha'awar taka
leda a gasar wasannin cin kofin zakarun nahiyar Turai (UCL) a kakar
wasannin badi, lamarin da ya tilasta Crystal Palace barin dan wasan ya
tashi daga kungiyar.
An yi kiyasin cewar darajar Zaha na tsakanin Yuro miliyal 65 zuwa 80 -
adadin kudin da ya yi daidai da tanadin da kungiyar Arsenal tayi domin
sayen dan wasan gaba idan ta samu nasarar zuwa gasar cin kofin UCL a
kakar wasannin badi.
Arsenal na fatan zuwa gasar UCL a kakar wasanni ta badi idan ta samu
nasarar doke kungiyar Chelsea a wasan karshe da zasu buga a gasar cin
kofin nahiyar Turai (UEFA) ranar Laraba mai zuwa.
Rahotanni sun bayyana cewar kungiyar Arsenal ta yiwa kungiyar Crystal
Palace tayin ba ta 'yan wasa uku da kudi domin daukan dan wasa Zaha.
Kungiyar tayi wannan tayin ne saboda ta rage yawan kudin da Crystal
Palace ke nema a kan dan wasan. Kungiyar Crystal Palace ta kafe a kan
cewar za ta sayar da Zaha ne kawai a kan farashin Yuro miliyan 80.
Yanzu dai Arsenal ta sanar da Crystal Palace cewar za ta bayar da 'yan
wasan ta guda uku; Reiss, Nelson da Carl Jekinson, da kuma Yuro miliyan
40 domin Zaha ya koma Emirata da taka leda.
Babu wata babbar kungiyar kasar Ingila da ta nuna sha'awar daukan dan
wasan, sai dai an bayyana cewar kungiyar PSG ta kasar Faransa da
Dortmund ta kasar Jamus na sansana dan wasan. Read more: https://hausa.legit.ng/1239121-kungiyar-arsenal-za-ta-bayar-da-yan-wasa-uku-da-kudi-don-daukan-dan-wasan-afrika.html

Legit Hausa
Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal dake kasar Ingila ta nuna
sha'awar bayar da 'yan wasan ta uku da kuma karin kudi domin daukan dan wasan
gaba na kungiyar Crystal Palace kuma dan asalin kasar Ivory Coast dake nahiyar
Afrika, Wilfred Zaha. Zaha, mai shekaru 26, ya samu nasarar saka kwallo 10 a
wasa 36 da ya buga wa kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace a kakar wasannin
bana.
A karshen watan jiya ne Zaha ya sanar da cewar yana da
sha'awar taka leda a gasar wasannin cin kofin zakarun nahiyar Turai (UCL) a
kakar wasannin badi, lamarin da ya tilasta Crystal Palace barin dan wasan ya
tashi daga kungiyar.
An yi kiyasin cewar darajar Zaha na tsakanin Yuro miliyal 65
zuwa 80 - adadin kudin da ya yi daidai da tanadin da kungiyar Arsenal tayi
domin sayen dan wasan gaba idan ta samu nasarar zuwa gasar cin kofin UCL a
kakar wasannin badi.
Arsenal na fatan zuwa gasar UCL a kakar wasanni ta badi idan
ta samu nasarar doke kungiyar Chelsea a wasan karshe da zasu buga a gasar cin
kofin nahiyar Turai (UEFA) ranar Laraba mai zuwa. Rahotanni sun bayyana cewar
kungiyar Arsenal ta yiwa kungiyar Crystal Palace tayin ba ta 'yan wasa uku da
kudi domin daukan dan wasa Zaha. Kungiyar tayi wannan tayin ne saboda ta rage
yawan kudin da Crystal Palace ke nema a kan dan wasan.
Kungiyar Crystal Palace ta kafe a kan cewar za ta sayar da
Zaha ne kawai a kan farashin Yuro miliyan 80. Yanzu dai Arsenal ta sanar da
Crystal Palace cewar za ta bayar da 'yan wasan ta guda uku; Reiss, Nelson da
Carl Jekinson, da kuma Yuro miliyan 40 domin Zaha ya koma Emirata da taka leda.
Babu wata babbar kungiyar kasar Ingila da ta nuna sha'awar
daukan dan wasan, sai dai an bayyana cewar kungiyar PSG ta kasar Faransa da
Dortmund ta kasar Jamus na sansana dan wasan.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi