Legit Hausa
A ranar Litinin ne wata kotun gwamnatin tarayya dake
zamanata a Owerri ta yanke hukuncin karbe kujerar majalisar wakilai ta mazabar
Nkwerre/Nwangele/Njaba?Isu daga hannun Ugonna Ozurigbo, dan takarar da aka bawa
shaidar ya ci zabe a karkashin inuwar jam'iyyar APC.
A sakin makon da ya gabata ne Ozurigbo ya yi murabus daga
mukaminsa na mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Imo. Da yake yanke
hukunci, Alkalin kotun, Jastis P. A. Rigime, ya umarci hukumar zabe ta kasa mai
zaman kanta (INEC) da ta janye shaidar cin zaben da ta bawa Ozurigbo tare da
mika ta ga Kingsley Echendu, dan takarar jam'iyyar PDP.
Jam'iyyar PDP da dan takarar ta basa cikin wadanda suka
shigar da kara kotu a kan zaben Ozurigbo. Kotun ta bayyana cewar Hariison
Nwadike, wanda ya shigar da kara, ne halastaccen dan takarar da ya lashe zaben
fidda 'yan takara na mazabar da jam'iyyar APC ta gudanar.
Nwadike ya shigar da karar jam'iyyar APC da hukumar zabe a
kan gabatar da sunan Ozurigbo ga masu zabe a matsayin dan takara bayan shine
wanda ya lashe zaben cikin gida. Saidai, bayan kotun ta yanke wannan hukunci,
Nwadike ya shaida wa manema labarai cewar duk da ya amince da hukuncin kotun a
kan cewar shine halastaccen dan takara, kuskure ne kotun ta bayyana dan takarar
jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya yi nasara.
Ya kara da cewa zai daukaka kara domin kalubalantar bangaren
hukuncin kotun da ya bayyana a mika kujerar ga dan takarar PDP, ya na mai
bayyana cewar kamata ya yi kotun ta bashi kujerar tunda dai shine halastaccen
dan takarar jamiyyar APC, wacce jama'a suka zaba
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi