• Labaran yau


  Kebbi: Tallafin N40m shugaban riko ya yi awon gaban kansa da N28m - Masu sayarwa da gyaran waya

  Mambabin kungiyar masu sayarwa da masu gyaran wayar salula na HADTEC a Birnin kebbi, sun zargi shugaban rikon kwarya na kungiyar Aliyu Muhammad Nassarawa wanda aka fi sani da suna Aliyu Tunga da yin awon gaban kansa da fiye da Naira Miliyan 28 daga cikin Naira Miliyan 40 da gwamnatin jihar Kebbi ta bayar rance da babu kudin ruwa ga masu sayarwa tare da gyaran waya a jihar Kebbi.

  A wata takarda da Layoyin shugabannin kungiyar reshen babban kasuwa na jihar Kebbi, Haliru Abdu da karamar hukumar Jega suka aika wa shugaban hukumar tsaro na DSS a jihar Kebbi ranar Alhamis.

  Takardar ta ce " Wadanda suka shigar da koke ta hannun mu suna zargin cewa a cikin watan Maris na 2019, mai girma Gwamnan jihar Kebbi Alh. Atiku Abubakar Bagudu ya bayar da bashi da babu kudin ruwa a ciki har N40.000.000.00m watau Naira Miliyan arba'in ta hannun Aliyu Muhammad Nassarawa saboda a raba wa yayan kungiyar HADTEC, amma bincike ya nuna cewa ya raba N11.370.750m ne watau Naira Miliyan goma sha daya da dubu dari uku da saba'in da dari bakwai da hansin kacal ga wadanda ya ga dama".

  Hakazalika, takardar ta ci gaba da cewa " Ranka ya dade, yana da muhimmanci a sani cewa sauran ragowar kudin N28.629.250m watau Naira Miliyan ashirin da takwas da dubu dari shida da ashirin da tara da dari biyu da hamsin ya yi awon gaban kansa ne da su".

  Bayanai sun ce yanzu haka, hukumar tsaro ta DSS a jihar Kebbi ta dukufa wajen binciken gaskiyar lamarin, da ma tarin korafe korafe da aka jera a kan lamarin kudin tallafin bashi da babu kudin ruwa da Gwamnatin jihar Kebbi ta ba masu harkar waya a jihar Kebbi.

  Kalli takardun koke a kasa:


  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kebbi: Tallafin N40m shugaban riko ya yi awon gaban kansa da N28m - Masu sayarwa da gyaran waya Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama