Legit Hausa
Tarayyar kasar Larabawa (UAE) tayi
sanarwa kan cewa duk wada aka kama d kallo da zai sa mata su kasance cikin rashin
walwala kaman kira da baki, kallo mai tsanani, ajiye lambobin waya da sauran su
zai fuskanci hukuncin zama a gidan yari tare da tara.
Khaleej Times ta rahoto cewa
rundunar yan sandan Dubai ta karfafa gargadi yayin da ta bada sanarwa cewa a
kwanakin nan ne ta kama mutane 19 bayan an kama su da laifin cin zarafin mata a
bakin teku da kuma hanyoyi.
A Kasar larabawa, wannan irin cin
zarafin har ila yau ya hada da kyafta musu ido, sumba da kuma yin maganganun
batsa. Daukan hotunan mata ba tare da izinin su ba yana daga cikin laifuffukan.
Darekta na kasa na sashin binciken
masu laifi, Birgadiya Jamal Salem Al Jallaf, yace mata suna da daman a basu
kariya da tsaro, ya kara da cewa wadannan irin laifuffukan cin zarafin sun saba
ma al’adun kasar larabawa.
Ahmad AlSayyed, babban lawya a
Charles Russell Speechlys da ke London, yace wannan irin laifin- ko da yake ba
babba ba ne - yana iya zuwa da hukuncin kora daga kasan. Lamarin yafi cikawa da
masu zuwa bakin teku don shakatawa.
Har ila yau, Legit.ng ta rahoto a
baya cewa Pope Francis ya sake gabatar da rokonsa don yafiya kan duk wani
rashin adalci a mulkin da mambobin coci da cibiyoyinta ke yi.
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi