Legit Hausa
Asiya El-Rufa'i, daya daga cikin matan gwamnan jihar Kaduna,
Malam Nasir El-Rufa'i, tare da dan ta na fuskantar barazanar dawo da su gida
Najeriya daga kasar Indonesia.
Asiya 'yar uwa ce ga fitacciyar 'yar jarida kuma 'yar
gwagwarmaya, Kadaria Ahmed. SaharaReporters ta wallafa cewar majiyar ta, ta
sanar da ita cewar duk da Asiya na da bizar shiga kasar, amma ta na fuskantar
matsala saboda rashin wata takarda.
Jaridar ta kara da cewa majiyarta ta sanar da ita cewar
gwamnatin Najeriya ta shiga tsakani domin warware matsalar da iyalin gwamnan ke
fuskanta a kasar Indonesia. "Yanzu haka gwamnatin Najeriya ta shiga
maganar kuma su na kokarin warware matsalar da gwamnatin kasar Indonesia,"
a cewar majiyar. Sai dai ba a bayyana me ya kai Asiya tare da dan ta kasar
Indonesia ba.
Kazalika babu wani jawabi daga gwamnatin jihar Kaduna ko
ofishin El-Rufa'i a kan abinda ya kai iyalin gwamnan kasar Indonesia ko kuma
karin bayani a kan matsalar da suke fuskanta. Ba bakon abu bane a wurin masu
mulki, musamman masu rike da mukaman siyasa, a Najeriya su fita kasashen ketare
tare da iyalinsu domin yawon bude ido ko duba lafiyar su. Ba kasafai yaran irin
wadannan mutane ke zama a Najeriya domin halartar makarantu ba.
Irin wannan hali na shugabannin mu ne yasa ragowar kasashen
duniya ke yiwa Najeriya kallon kaskanci da raini da kuma nuna shakku a kan
niyya da ikirarin shugabannin kasar mu na kawo gyara a harkokin kasar, musamman
bangaren kiwon lafiya da inganta ililmi.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Tags:
LABARI