Kai tsaye: Bikin rantsar da shugaban kasa da mataimakinsa


Legit Hausa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauki rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasar Najeriya a karo na biyu a yau Laraba, 29 ga watan Mayu. Shugaban alkalan Najeriya, Justis Mohammed Tanko ne ya rantsar da shugabannin biyu. A yanzu haka, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Oinbajo ya dauki rantswar kama aiki a karo na biyu.

Farfesa Shehu Galadanci ne zai bude taron rantsa da shugabannin da addu'ar addinin Musulunci. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa dandalin Eagle Square da ke Abuja, inda za a rantsar da shi tare da Mataimakinsa Yemi Osinbajo a wa'adin mulki na biyu. Mataimakin shugaban kasa, Osinbajo ma ya isa dakin taro na Eagle Sqare.

Tsohon Shugaban kasa a mulkin soja, Janar Yakubu Gowon da tsohon Shugaban kasa, Cif Ernest Shonekan na daga cikin manyan mutanen da suka isa filin taro na Eagle Square a Abuja, wajen bikin rantsar da Shugaban kasa a yau Laraba, 29 ga watan Mayu. 

Za a rantsar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo a wajen taron. Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa har yanzu tsoffin Shugabannin kasa Olusegun Obasanjo da Ibrahim Badamasi Babangida basu hallara ba a wajen taron. 

Sauran manyan mutanen da suka hallara sun hada da mambomin kungiyar sojojin diflomasiyya, manyan yan kasuwa, Aliko Dangote, gwamnoni, jiga-jigan jam’iyyar All Progressives Congress (APC), yan majalisa da sauransu. An tattaro cewa an tsaurara matakan tsaro a wajen taron.
A baya Legit.ng ta rahoto cewa ma’aikatan FRSC akalla 2000 za a jibge a cikin babban birnin tarayya Abuja a dalilin bikin rantsuwar da ake yi yau Laraba 29 ga Watan Mayu. 

Wani babban jami’in hukumar FRSC masu kula da tituna a Najeriya, Mista Gora Wobin, ya bayyana cewa za a baza ma’aikata da za su lura hanyoyi a yayin da ake sake rantsar da shugabannin Najeriya.
 

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN